Kafin neman littafi a lura da wadannan bayanai muhimmai:

1. Saboda kasancewar wannan cibiyar ta isar da sako ce kawai; don haka ana aikawa da littattafai na addini ne a fagen mazhabar Ahlul-baiti (a.s) kawai. Don haka muna bayar da uzuri ga masu neman littattafai Irfani, Falsafa, Adabi, Siyasa, da sauran fagagen da ba su shafi isar da sakon mazhaba ba.

2. Idan kun samu littattafanmu bisa kuskure, to sai ku aiko mana da bayani ta imail.

3. Ku kula sosai wurin zabar yare, domin ana aika littattafai bisa la'akari da yaren da kuka zaba ne kawai.

4. Bisa la'akari da cewa ana bugawa kuma a yada mafi yawan littattafan da kuke nema wajen Iran ne, kuma akwai wahalar samun wasu daga cikinsu a cikin kasuwannin Iran; don Allah muna neman ku nemi aiko muku littattafan da suka shafi (Akida, mahdiyanci, tarihin musulunci, halaye, da ) ne kawai.

5. Idan littattafan da ka samu ba su yi maka ba, ba su burgi ka ba, bai halatta ba ka ajiye su a gida ba tare da karantawa ba, don haka dole ne ka ba wa masu bukatar su.

6. Ku rubata sunayenku cikakku hada da sunaye na biyu a fom din da kuke cikewa, domin kada a samu matsala lokacin da zaku karba a post ofis.

7. Ku sanya lambar waya, da imel, da kuma adres na post ofis da yake aiki.

8. Wannan cibiya ba ta iya aikawa da littafi sama da sau daya, don haka ba ta sauraron neman aika littattafai na biyu.

9. Yana da kyau mai neman aika masa littafi ya sanya wani dan bayani a cikin wasikar tasa da yake bayanin matsayin ilminsa da matakin iliminsa, da kuma yanayin addini a kasarsa, da kuma 'yan shi'an da suke yankinsa.

10. Dole ne matuka lallai a sanar da mu isar littattafan da muka aika bayan an karba

11. Bayan an karbi littattafan yana da kyau ku aiko mana da mahangarku, da gyaranku, domin mu sani.

Click Here